ApkDownload

Sheikh Jafar Mahmoud Juz Amma Quran Offline APK

Latest Version 2.2 for Windows
Updated 2020-05-13

App information

Version 2.2 (#1004)

Updated 2020-05-13

APK Size 32.3 MB

Requires Android Android 4.1+ (Jelly Bean)

Offered by engrgwarzo

Category Free Lifestyle App

App id com.andromo.dev653901.app643370

Developer's notes Karatun sheikh jafar mahmud juz Ammah wanda baya bukatar internet ko data.

Screenshot

Click on the image to see full size

Editor's review

Download the latest Sheikh Jafar Mahmoud Juz Amma Quran Offline application, version 2.2, compatible with Windows 10/11 (using emulators such as Bluestacks), Android devices. This free Lifestyle app is developed by engrgwarzo and is easy to download and install.

Previous versions, including 2.2, are also available. If you need help or have any problems, please let us know.

Description

wannan application din free ne wanda ya kunshi karatu na juz ammah na marigayi sheikh jafar mahmud adam kano wato audio mp3,yana dauke da sauti mai kyau kuma shi ba sai da data ko internet yake aiki bah,ina fatan zakuyi downding dinsa cikin sauki,sannan muna adduar Allah ya jikan malam da rahamah.

Tarihin Sheikh Jafar MahmudAdam***
An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964).Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da
Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano. Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.Bayan da Malam ya kamala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen
kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (EgyptianCultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin
shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da
daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya kamala wadannan makarantu a shekara ta 1983.Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an,wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take Khartoum, Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar,Sheikh Abdul-Aziz Ali al-
Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansulittattafai na hadisi a gurinsa,da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin malamansa na jami'a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy. Malam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi.Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka Haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi. Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna. Ameen
Da fatan zakuji dadin wannan application wanda ba saida internet ba ko data,dan Allah abawa yan uwa musulmai da dangi,nagode.

App permissions

Sheikh Jafar Mahmoud Juz Amma Quran Offline 2.2 APK requires following permissions:

Allows using PowerManager WakeLocks to keep processor from sleeping or screen from dimming.

Allows an application to write to external storage.

Allows an application to read or write the system settings.

Allows applications to open network sockets.

Allows applications to access information about networks.

Allows an application to read from external storage.

Ratings and Reviews

Rating: 5.0/5 based on Less than 100 reviews

(*) is required

Previous versions

Sheikh Jafar Mahmoud Juz Amma Quran Offline 2.2 APK for Windows (#1004, 32.3 MB)